Sarki Charles zai yi tozali da William Ruto
October 27, 2023Tsawon kwanaki biyu na ziyarar Sarki Charles III zai gana da bangarori daban-daban ciki har da kamfanoni da matasa da jagororin addinai, kana zai ziyarci yankin Mombasan kudancin Kenya don ganewa idonsu wuraren bude ido na gandun daji.
Karin Bayani: Sarki Charles na Ingila na ziyara a Faransa
Daman Kenya na da mummunan tarihi ga iyalan gidan sarautar Biraniya, inda a can ne ma Sarauniya Elizabeth ta ji rasuwar mahaifinta Sarki Georges na VI a shekarar 1952.
Karin Bayani: An nada Sarkin Ingila bayan shekaru 70
Masana na hasashen babban batun da zai fi daukar hankalin zaiyarar ta Sarki Charles ba zai wuce na karfafa kungiyar hadakan kasashen Renon Ingila ta Commonwealth da ke cikin wani tangal-tangal a yayin tattaunawarsu da shugaban Kenyan William Ruto.