Bincike ya ce Yariman Saudiya na da hannu a kisan Khashoggi
June 19, 2019A wani rahoto da Agnes Callamard, mai bincike ta Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar, ta nemi a sanya takunkumai kan kaddarorin Yariman Saudiya mai jiran gado Mohammed bin Salman da ya mallaka a kasashen waje har sai lokacin da ya aka iya wanke shi daga zargin kisan dan jarida Jamal Khashoggi.
Callamard da ta jagoranci binciken da Majalisar ta gudanar, ta ce sakamakon bincike ya sami kwararan hujjoji da suka tabbatar da hannun Yariman a kisan amma kuma da kwararran hujjojin da aka samu akwai bukatar gudanar da wani bincike na gaskiya.
A watan Oktobar bara, dan jaridan da ya sha sukar manufofin Saudiya ya gamu da ajalinsa a karamin ofishin jakadancin kasar da ke Turkiya, an gano yadda wasu jami'an kasar suka aikata kisan a cikin ofishin. Tun kuma wancan lokacin aka soma zargin Bin Salman, sai dai mahukuntan Saudiyyan sun tsaya kai da fata inda suka nesanta Yeriman da hannu a kitsa kisan Khashoggin.