Ma'aikatan Twitter na yi wa jama'a kutse
November 7, 2019Talla
Masu shigar da kara sun ce sun gano yadda aka yi hayan wadannan kwararrun kamfanin, domin su yi ta sa ido kan shafukan wasu fitattun mutane da ake ganin na yawan sukar manufofin gwamnati. Sun ambato wani da ke da masu binsa fiye da miliyan daya a Twitter da kuma wani fitacce dan jarida, ba tare da an baiyana sunayensu ba, da aka ce suna daga cikin wadanda Saudiyyan ta bayar da izinin a saka wa ido sosai.