1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta yi barazanar yanke kauna da Amirka

Ramatu Garba Baba
December 17, 2018

Masarautar Saudiyya ta yi watsi da kudirin dokar da 'yan majalisar dattawan Amirka suka zartar na neman hukunta Yerima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa zargin kisan Jamal Khashoggi.

https://p.dw.com/p/3AE8m
Mohammed bin Salman al-Saud ist der Kronprinz, Verteidigungsminister und stellvertretende Premierminister Saudi-Arabiens
Hoto: picture-alliance

'Yan majalisar dattawan sun nemi gwamnatin Amirka ta gaggauta janyewa daga yakin Yemen da ke ci gaba da lakume rayukan fararen hula. A martanin masarautar, ta zargi Amirka da shiga hurumin da ba nata ba, ta kuma yi barazanar yanke kauna da Amirka akan wannan batu.

Wannan na zuwa ne bayan da akasarin 'yan majalisar dattawan na Amirka suka amince da kudirin doka, da za ta bayar da damar hukunta Yerima Salman bisa rawar da ya taka a kisan Khashoggi da aka yi a karamin ofishin jakadancin kasar da ke a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a watan Oktobar da ya gabata, tare da ganin Amirka ta kuma janye duk wani goyon bayan da ta ke bai wa Saudiyyan a yakin da take jagoranta a kasar Yemen.