1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta karyata mutuwan bin laden

Zainab A MohammadSeptember 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bty2

Saudi Arabia ta karyata zargin da ake,nacewa shugaban kungiyar Al qaeda Osama bin Laden ya rasu,wanda ke dada kawo shakku dangane da wasu bayanan sirri da suka bulla a faransa,kancewa hukumar leken asirin saudiyyan tayi imanin cewa,ya rasu a watan daya gabata.Hukumomin faransa dana Amurkan tun a jiya dai sukace basu da wani tabbaci a dangane da rahotannin jaridun faransa,dake nuni da mutuwan Bin Laden a karshen watan Augusta a kasar Pakistan.Sakamakon hakane ofishin jakadancin Saudi Arabia dake Washinton ya gabatar da wata sanarwa dake nuni dacewa,masarautar kasar bata da wani shaida dake tabbatar da mutuwan osama bin laden,dangane da rahotannin kafofin yada labaru.