Saudiyya ta rataye wani dan Pakistan
February 12, 2015Hukumomin Saudiyya sun rataye wani dan Pakistan kai sakamakon yanke masa hukuncin kisa da aka yi bayan da aka same shi da laifin safarar miyagun kwayoyi. Shi dai Babir Isaac, shi ne mutum na 29 da aka aiwatar da hukuncin kisa a kansa a Saudiyya tun daga farkon wannan shekara i zuwa yanzu.
Kungiyoyin duniya da suka himmatu wajen kare hakkin dan Adama suna ci gaba da yin tir da dokokin na Saudiyya da suka tanadi kisa idan aka same mutum da wani mummunan laifuka ,ciki har da fyade da kisan kai da yin ridda da kuma saye ko sayar da miyagun kwayoyi.
A watan Satumba na shekarar da ta gabata, wani kwararren jami'i na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana fargabar game da yadda shari'a ke gudana a wannan kasa, tare da yin kira ga Saudiyya da ta jingine shari'ar musulunci wajen yanke hukunci.