1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya: Yaki a kan 'yan Shi'a marasa rinjaye?

Abdullahi Tanko Bala ATB
August 10, 2017

A kasar Saudiyya tsawon watanni uku ke nan ana fafata mummunan fada a garin Awamiyya da ke gabashin kasar, amma an hana masu daukar rahotanni shiga yankin.

https://p.dw.com/p/2i2In
Screenshot Twitter Saudi Arabien Zerstörung der Stadt Awamiya
Hoto: Twitter/trbrtc

Hotunan tauraron dan Adam da aka dauka sun nuna irin yadda aka ragargaza dukkan gundumomi da ke birnin. Ko da yake an yada wasu daga cikin hotunan ta'asar a shafukan sada zumunta, lamarin ya kasance da matukar wahala a iya samun bayanai daga kafofi masu zaman kansu. Hatta 'yan jaridu na kasashen waje an hana musu damar shiga yankin.

Tsakiyar inda ake wannan gumurzu dai shi ne Al-Masora, yanki mai tarihi na Awamiyyawa. An yi dauki ba dadi a titunan birnin tsakanin mayakan Shi'a da sojojin Saudiyya. Mutane akalla 15 suka rasa rayukansu a kawanyar da dakarun na Saudiyya suka yi wa Awamiyya, inda aka yi amfani da manyan makamai. An wallafa wasu tankokin yaki kirar kasar Kanada a shafukan sada zumunta wadanda aka yi amfani da su wajen yin dirar mikiya a kan jama'a fararen hula a garin. A kan haka ne jama'a a Ottawa babban birnin kasar Kanada suka yi kiran gwamnati ta dakatar da sayar da makamai ga Saudiyya.

Rusau da sauyin matsuguni ba bisa ka'ida ba

Makasudin tashin hankalin dai shi ne shirin Saudiyya na rushe tsohon garin da ya samo asali shekaru 400 da suka wuce domin gina rukunin kantuna na zamani, lamarin da mazauna yankin suka ce ba su lamunta ba. A watan Afrilun da ya gabata Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Saudiyya ta dakatar da tilasta sauya wa mutanen kauyen matsuguni da kuma rushe gidajen nasu.

Screenshot Twitter Saudi Arabien Zerstörung der Stadt Awamiya
Hoto: Twitter/trbrtc

A wata ganawa da tashar DW Sebastian Sons wani kwararre kan al'amuran Gabas ta Tsakiya a cibiyar nazarin harkokin waje ta Jamus ya nuna shakku game da ikirarin gwamnatin Riyadh cewa tana so ne ta samar da kayayyakin bukatu domin inganta rayuwar mazauna yankin.

"A hukumance abin da gwamnatin Saudiyya ke cewa shi ne za a sake gina sabbin gidaje domin raya yankin na Awamiyya don jin dadin jama'ar yankin, amma a waje guda ana gani akwai wata a kasa. Hakan kuwa na nufin cewa za a dakile 'yan Shi'a wadanda suke marasa rinjaye tare da mayar da su saniyar ware, irin tafarkin da Saudiyya ta sha yi tsawon shekaru gommai."

Keta hakkin marasa rinjaye

Danniya da mayar da mabiya Shi'a saniyar ware ta dade da zama tushen rikicin. Kashi goma cikin dari ne dai 'yan Shi'a daga cikin al'ummar Saudiyya miliyan 30. Galibi 'yan Shi'ar suna zaune ne a gabashin kasar, inda Saudiyyar ke da albarkatun mai. Sai dai kuma yan Shi'ar ba su da wani anzigo a harkokin rayuwa kamar yadda ba kasafai ake damawa da su a harkokin mulki da siyasar kasar ba.

Irak Proteste gegen die Hinrichtung von Nimr Al-Nimr in Saudi Arabien
Zantar da hukuncin kisa a kan Nimr Al-Nimr a Saudiyya ya sha tofin Allah tsine daga 'yan Shi'aHoto: Reuters/T. Al-Sudani

Bugu da kari suna fuskantar matsi da bambancin akida, kasancewar 'yan Sunni wadanda suke da rinjaye suna bin tafarkin Wahabiyanci ne wanda yan Shi'ar ke yi wa kallo a matsayin wadanda ba Musulmi ba.

Garin Awamiyya dai nan ne mahaifar Nimr al Nimr fitaccen malami Shi'a da Saudiyya ta zartarwa da hukuncin kisa a shekarar 2016 kan zargin ta'addanci.

Ali Adubusi na kungiyar kare hakkin bil Adama ta hadakar tarayyar Turai da Saudiyya wanda ya fito daga yankin Awamiyya da ke gudun hijira a birnin Berlin a nan Jamus ya yi karin haske game da garin.

"Ggarin ya kasance cibiyar adawa da gwamnati tun bayan guguwar sauyi a kasashen Larabawa, kuma tun daga wannan lokaci Saudiyya ke amfani da karfi da tursasawa a kan duk mai adawa da ita har kawo yanzu."

A karshe dai gwamnatin Saudiyyar na iya yin nasarar cimma burinta na rusau da sauyin matsuguni ko da kuwa bai yi wa jama'ar dadi ba.