Saudiyya:Sauraron shari'ar kisan Khashoggi
January 3, 2019Mutanen da ake zargin sun hallara a kotu tare da Lauyoyinsu. Tun da fari dai babban lauyan gwamnatin ya baiyana cewar sau biyu Saudiya ta nemi kasar Turkiya ta gabatar mata da shaidun da ta mallaka na kisan dan Jaridar, batun da Istanbul ta yi watsi da shi.
Har ya zuwa wannan lokaci dai ba'a sanar da sunayen mutanen goma sha dayan da ake tuhuma ba. Jamal Khashoggi mai shekaru 59 ya rasa ransa a yayin da yaje neman takardun izinin aure a karamin ofishin jakadancin Saudiyar da ke Istanbul.
Turkiya ta nemi a gudanar da shari'ar wadanda ake zargin a kasarta, batun da Saudiyya taki amincewa. Hukumar leken asirin Amirka CIA ta zargi Yarima Muhammed bin Salman da bada umarnin kisan dan Jaridar koda yake tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, babban mai shari'ar kasar ta Saudiyya ya wanke Yariman daga zargin kisan kan.