Talla
Shugaban Amirka mai jiran gado Donald Trump a wata hira da yayi da mujallar Bild ta nan Jamus ya jaddada ikrarin da ya yi a lokacin zabe na janye kasarsa daga kungiyar kawancen tsaro ta NATO yana mai cewa kungiyar ba ta wani alfanu. Wadannan kalamai dai sun haifar da damuwa da kuma ayar tambaya daga masharhanta da dama a cikin kungiyar ta NATO da kuma kungiyar tarayyar Turai.