A cikin shirin za'a ji a Najeriya bangaren zartarwa na gwamnatin tarayya ya shigar da kara gaban kotun koli domin neman fassarar doka ta nadin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, yayin da majalisar dattijai ke cewa ita ce ke da ikon tantance shugaban kafin a iya tabbatar da nadinsa a kan mukamin a hukumance.