A cikin shirin za ku ji cewa an rantsar da sabon shugaban Amirka Donald Trump, shugaba na 45 a jerin shugabannin kasar inda a jawabinsa ya jaddada cewa daga yanzu zai maida hankalinsa ne ga bada fifiko ga bukatun Amirka da Amirkawa a ayyukan da zai sanya a gaba don ci gaban Amirka.
https://p.dw.com/p/2WA1r
Talla
Kamar yadda aka saba bisa al'adar Amirka, bikin rantsuwar ya samu halartar tsoffin shugabannin kasar. A daura da bikin rantsuwar masu adawa da shugaba Trump sun gudanar da zanga zanga sai dai yan sanda sun tarwatsa su.