1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iskar Carbon babbar barazana ga Amirka

Yusuf Bala Nayaya MNA
November 24, 2018

Wani rahoto daga kafar gwamnatin Amirka ya yi gargadi na cewa sauyin yanayi zai ci gaba da illa ga muhalli da tattalin arziki da batu na lafiya ga al'umma a Amirka, muddin ba a dauki matakai ba na rage iskar Carbon.

https://p.dw.com/p/38qTS
USA Waldbrände in Kalifornien
Hoto: picture-alliance/AP Photo/N. Berger

A cewar cibiyar da ke nazartar sauyin na yanayi a mataki na hudu a Amirka idan ba a daukar matakai na kokarin rage abubuwan da ke lalata muhalli a Amirka, sauyin yanayin zai kawo asarar dukiyoyi, abin da zai yi illa ga fafutukar habbaka tattalin al'umma a sama da shekaru 100.

Rahoton ya nunar da yadda karuwar zafi ke illa ga aikin gona da ja'izar ambaliya da wutar daji da ma bazuwar wasu cututtuka irin na yankin Tropics a kasar ta Amirka.

Wannan rahoto dai ya yi karo da manufofin Shugaba Donald Trump da ke bayyana sauyin yanayin da zama shaci fadi inda ma ya fice daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris mai kuduri na rage karuwar zafi a duniya.