1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sauyin yanayi na duniya a Amirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 23, 2019

Majalisar Dinkin Duniya za ta kara matsa lamba ga kasashen duniya, su dauki matakan kare muhalli gabanin taron sauyi ko kuma dumamar yanayi na duniya da zai gudana a kasar Chile cikin watan Disambar wannan shekara.

https://p.dw.com/p/3Q6cA
USA Greta Thunberg in NewYork
Greta Thunberg deltar på FN klimat toppmöte för unga i...
Dalibai mai rajin kare muhalli Greta Thunberg tare da Sakatare Janar na majalisar António GuterresHoto: picture-alliance/TT NYHETSBYRÅN/P. Lundahl

Sakatare Janar na majalisar António Guterres ne ya bayyana hakan a jawabin da ya yi, yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniyar kan sauyin yanayi da ke gudana a yanzu haka a birnin New York na Amirka. Jawaban na Guterres dai na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar barazanar rushewar yunkurin yaki da dumamar yanyin. Tuni ma dai dalibar nan mai fafutukar yaki da sauyin yanayin 'yar kasar Sweden Greta Thunberg da ta kirkiri gangamin "Fridays for Future" domin kare muhalli, ta halarci taron tare da gabatar da jawabi mai sosa rai dangane da yadda shugabanni ke rikon sakainar kashi da batun na sauyin yanayi da ta ce yana da matukar illa ga rayuwa.