1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sayen kuri'un masu zabe a Ghana

November 29, 2016

A daidai lokacin da zaben shugaban kasa ke dada karatowa a Ghana, wasu 'yan kasar na neman 'yan siyasa su biya kudi domin su kada musu kuri´a, saboda a cewar su lokaci ne na jama´a su samu rabonsu.

https://p.dw.com/p/2TRwV
Präsidentschaftswahl Ghana 2012
Hoto: AFP/Getty Images

"Tabbas zan sayar da kuri´ata idan na samu me saya, maganar gaskiya kuri´ata ta sayarwa ce, yanzu haka ma ina neman mai saya ne, saboda ´yan siyasa basu da tabbas, idan ka zabe su baza ka sake ganin su ba."

'Yan kasar ta Ghana basu da yakinin siyasar akida a wannan karon zatayi tasiri, saboda yadda suke rububin cefanar da kuri´ar su.

Shi ma wannan cewa yake "zan sayar da kuri´ata, ana sayen duk kuri´a daya kan kudi cedi 1000 na Ghana, saboda ban san wanene zai zama shugaban kasa ba, abu ne mai sosa rai irin yadda yan saiyasar mu suka zama, kuri´ata ta sayarwa ce, cedi 1000 ne kacal.

Wadannan dai basu boye ba, sun fito fili sun bayyana sayar da kuri´ar su tamkar wata haja, al´amari ne dake nuna cewa wadda ya saya da daraja to shine zai samu kuru´u mafi rinjaye a zaben na Ghana. To amma a cewar Paul Osei Kuffour masanin kimiyar siyasa ne, dake aiki da cibiyar cigaban demokaradiya a birnin Tamale, yace wannan wani babban koma baya ne ga tsarin gudanarwar kasar.

"Saboda me zaka yasar da kuri´ar ka, me yasa zaka bari a saye ka. Wannan koma bayane ga tsarin demokaradiyya. Kuma hakan na nufin abinda jama´a suka zaba bazai kasance hakikanin gaskiyar abinda mafi yawan jama´a suka zaba ba"

Yan kasar Ghana da dama na cigaba cin kasuwar cefanar da kuri´un su. Kwanaki biyu da suka gabata, yan siyasa sun yiwa jama´ar birnin Tamale ruwan kudi da atamfofi. Nabari Abdullai wani wani amshakin dan siyasa ne, ya bayyana dalilin da yasa jama´a ke sayar da kuri´ar su.