SiyasaJamus
Scholz da Putin sun tattauna, karon farko cikin shekaru biyu
November 15, 2024Talla
Kakakin gwamnatin na Jamus ya ce Scholz da Putin sun yi tattaunawa ta tsawon awa guda.
An nruwaito cewa Scholz ya bukaci Putin ya shiga tattaunawa don samun zaman lafiya mai dorewa da Ukraine.
Haka kuma kakakin gwamnatin ya ce Scholz ya tattauna da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy, kuma shugaban gwamnatin na Jamus ya jaddada kudirin kasarsa na ci gaba da taimaka wa Ukraine komai tsawon lokaci.