SiyasaTurai
Scholz: Gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da ayyukanta
November 28, 2023Talla
Wannan matsala dai ba za ta shafi kudaden da ake kashewa a yanzu ba, inda Olaf Scholz ya tabbatar wa 'yan majalisar dokoki ta Bundestag a wannan Talatar (28.11.23) cewa, gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da ayyukanta.
Sai dai jawabin shugaban gwamnatin na Jamus, ya gaza fayyace yadda za a shawo kan matsalar wagegen gibin, bisa ga hukuncin da wata babbar kotun kasar ta yanke a farkon wannan watan ba, wanda ya janyo suka daga jam'iyyun adawa.
Ya tabbatarwa da Jamusawa cewar, ko kadan hukuncin kotun tsarin mulkin, ba zai canza komai ba a rayuwarsu ta yau da kullum, a yanzu da ma nan gaba, a bangaren tallafin yara ko tallafin karatu da fensho ko tallafin biyan haya.