Schulz zai kalubalanci Merkel a zaben kasa
January 24, 2017Talla
Tsohon shugaban majalisar dokokin tarayyar Turai Martin Schulz ya shirya jagorantar jam'iyyarsa ta Social Democrats SPD domin kalubalantar shugabar gwamnati Angela Merkel a zaben kasa da za'a gudanar a watan Satumba.
Tasayar da Schulz domin yin takarar dai ya biyo bayan sanarwar da shugaban jam'iyyar Sigmar Gabriel ya yi ne a yau Talata cewa zai sauka daga shugabancin jam'iyyar ya kuma bada shawarar tsayar da tsohon jami'in diplomasiyyar a Brussel domin zama dan takara a mukamin shugaban gwamnati kuma shugaban jam'iyyar SPD.
Kasancewar Gabriel na bayan Merkel a kuri'ar goyon bayan jama'a, yan SPD da dama sun yanke kaunar cewa ba zai yi wani tasiri wajen daga martabar jam'iyyar. ba.