Kotu ta yanke wa madugun adawan Senegal hukunci
March 30, 2023Bayan daurin talala na watanni biyu Ousmane Sonko zai biya tara ta miliyan 200 na kudin cfa watau yuro dubu 300 kan laifin yin kalamen karya da cin mutumcin wani minista.
Sai dai jim kadan bayan sanar da sakamakon shari'ar lauyoyin da ke kare Sonkon sun shaida wa kafanin dillacin labarun Faransa na AFP cewa ko kadan hukuncin da aka yanke masa ba zai shafi tsayawa takararsa a zaben kasar da ke tafe a shekarar 2024 ba.
Mai shekaru 48 da haihuwa Ousmane Sonko na a matsayin babban abokin hamayar shugaba mai ci Macky Sall wanda nuna alamun tsayawarsa takara a karo na uku da masu adawa da shi ke ganin ya sabawa dokokin kasar ya tayar da gagarumar kura a fagen siyasar Senegal inda 'yan adawa suka yi ta yin bore na kalubalantar matakin shugaba Sall.