Wani dalibi ta mutu a taho mu gama da jami'an tsaron Senegal
February 10, 2024Talla
Jami'an tsaron sun yi amfani da karfi da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa dandazon matasan da suka fito zanga-zanga.
Daruruwan masu boren ne aka ce bayan hatsaniyar ta barke suka yi ta jifar 'yan sanda da duwatsu.
Boren na jiya Juma'a ya yi sanadiyar rufe manyan hanyoyin birnin Dakar da na zirga-zirga jirgin kasa gami da kasuwanni.
Ko baya ga birin Dakar, an gudanar da zanga zanga a wasu biranen kasar, inda can ma jami'an tsaro suka yi amfani da borkonon tsohuwa wajen koran jama'a.
A farkon makon nan ne dai mahukunta a Senegal a karon farko suka sanar da dage zaben shugaban kasa, matakin da ya fusata al'umma.