1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Senegal ta bai wa Sonko 'yanci

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 15, 2023

Lauyoyin gwamnatin Senegal sun ce suna shirin daukaka kara, dangane da hukuncin da kotu ta yanke na a saki jagoran adawar kasar da ke tsare a gidan kaso Ousmane Sonko a kuma sake ba shi damar tsayawa takara.

https://p.dw.com/p/4aDmi
Senegal | Jagora | Adawa | Ousmane Sonko
Jagoran adawar Senegal Ousmane Sonko ya yi nasara a kotuHoto: Seyllou/AFP

Wannan hukuncin dai, zai bai wa jagoran adawar kasar ta Senegal da ke tsare a gidan kaso Ousmane Sonko damar tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a badi. Mai shekaru 49 a duniya Sonko wanda aka bayyana da bai cancanci tsayawa takara ba bayan da aka iza keyarsa gidan kaso a watan Yunin wannan shekara, yana da wa'adin nan da ranar 26 ga wannan wata na Disamba da muke ciki ya tattara tare da mika duk wasu takardunsa na neman tsayawa takara a zaben watan Fabarairun shekara mai zuwa ta 2024.