Madugun adawan Senegal zai sake gurfana a kotu
April 29, 2023Lauyan da ke kare matar da ake zargin Sonko da yi wa fyade shi ne ya sanar wa manema labarai cewar madugun adawan zai sake bayyana a gaban kotun birnin Dakar a ranar Talata 16 ga watan Mayu inda za a ci gaba da saurarensa.
Wannan dai ita ce tuhuma ta biyu da ake yi wa Ousmane Sonko bayan tuhumar farko kan zarginsa da furta kalaman karya ga wani minista inda kotu ta yanke masa hukuncin daurin talala na watanni biyu tare da biyan tara ta miliyan 200 na kudin cfa kwatankwacin yuro dubu 300 hukuncin da a cewar lauyoyinsa ko kadan ba zai shafi tsayawa takararsa a zaben kasar da ke tafe a shekarar 2024 ba.
Mai shekaru 48 da haihuwa Ousmane Sonko na a matsayin babban abokin hamayar shugaba mai ci Macky Sall wanda nuna alamun tsayawarsa takara a karo na uku ya tayar da gagarumar kura a Senegal din inda 'yan adawa suka yi ta yin bore na kira shugaban da ya mutumta kundin tsarin mulki wanda ya haranta masa sake tsayawa takara bayan wa'adin mulki biyu.