Dan Ukraine ya samu lambar yabo
October 25, 2018Talla
Sentsov mai shekaru 42 an haisfeshi a birnin Simferopol da ke cikin yankin Kirimiya, ya yi fafutukar ganin an sako fursunonin siyasar Ukraine da ke daure a Rasha. Matashin ya shahara wajen sukar gwamnatin Rasha kan mamaye yankin Kirimiya da karfin tuwo.
Wannan ya bashi damar shiga sahun mutane uku da suka haye mataki na karshe a cin kyautar, ciki har da wasu kungiyoyi 11 masu ceto 'yan ci rani a teku, tare da Nasser Zefzafi jagoran gwagwarmayar kwato 'yanci a Maroko da ya shafe shekaru 3 a daure.
Kyautar Sakharov na zuwa da tukuicin kudi na dala dubu hamsin, Nelson Mandela shi ne mutum na farko da ya taba lashe kyautar tun bayan da aka soma bayarwa a shekarun 1988.