1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi akan taron London dangane da Libiya

March 30, 2011

A jiya talata ne aka gudanar da taron ƙasa da ƙasa akan makomar Libiya bayan Ghaddafi. An kuwa lura da saɓanin dake tsakanin ƙasashen taron dangin in ji Daniel Scheschkewitz a cikin wannan sharhi nasa

https://p.dw.com/p/10kuQ
Mahmoud Jibril shugaban majalisar gwamnatin riƙon ƙwarya ta LibiyaHoto: picture-alliance/dpa

A taron da suka gudanar a birnin London a jiya talata, wakilai na ƙasa da ƙasa, sun yi alƙawarin ba da tallafin kuɗi ga gwamnatin wucin gadi da 'yan tawayen ƙasar Libiya suka naɗa. An dai yi iƙirarin cewar ana shirye-shirye ne ga makomar Libiya bayan gushewar Gaddafi daga karagar mulki. To sai dai kuma har yau akwai saɓani tsakanin su kansu ƙasashen dake wa Libiya taron dangi akan alƙiblar da aka fuskanta don cimma wannan manufa. Gaba ɗaya dai taron dangin na ƙasa da ƙasa ya samu kansa a cikin wani hali ne na tsaka mai wuya.

Fatan kafa turbar demokraɗiyya a Libiya

Ägypten Libyen Arabische Liga Ban Ki Moon in Kairo
Sakatare-janar na Majalisar Ɗinkin Duniya na fafutukar girka dimokraɗiyya a LibiyaHoto: dapd

A dai cikin sanarwar bayan taron da aka bayar an yi nuni ne da cewar ana fatan gina wata 'yantacciyar ƙasa ta Libiya da zata haɗe ƙarƙashin tutar demokraɗiyya. To amma fa babu wata alamar dake yin nuni da cimma wannan manufa nan ba da daɗewa ba ta la'akari da matakan soja da na siyasa da kuma diplomasiyyar da ake ɗauka. Ƙasashen dake ƙawancen, waɗanda suka hallara a birnin London jiya talata, duka-duka wata 'yar ƙaramar manufa ce suka dace akanta. Taron ya amince ne cewar wajibi ne a kafa wani kwamitin tuntuɓa na ƙasa da ƙasa, wanda zai yi bakin ƙoƙarinsa wajen girka turbar demokraɗiyya a Libiya bayan gushewar Ghaddafi. To amma fa ba a samu daidaituwa tsakanin mahalatra taron ba a game da yadda za a tilasta wa madugun juyin juya halin na Libiya ya kakkaɓe hannunwansa daga al'amuran mulki. Faransa dai ta bayyana muradinta na yi wa 'yan tawayen ɗamarar makamai, lamarin da Birtaniya a nata ɓangaren ta ga tamkar neman wuce gona da iri ne. Ita kuwa Amirka, a ganinta babban abin da aka sa gaba shi ne kifar da mulkin Ghaddafi, amma kuma tana adawa da tura dakarun mayaƙa na ƙasa zuwa Libiya. Ita kuma ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO, wadda ke jan akalar matakan na soji ta ruwa da sama, ta ce zata yi biyayya ne sau da ƙafa ga ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya. Jamus, wadda ba ta da hannu a matakin na soja cewa tayi, a shirye take ta taimaka wa Libiya wajen girka demokraɗiyya bisa manufa.

Mai yiwuwa da hannun Alƙa'ida da Hizballah a tawayen

Krieg in Libyen
'Yan tawayen Libiya na ƙoƙarin mamayar Ras LanufHoto: AP

A nasu ɓangaren kuwa 'yan tawayen na Libiya dake bakin ƙoƙarinsu wajen neman goyan-baya daga ƙetare na ci gaba da iƙirarin cewar su masu sha'awar mulkin demokraɗiya ne tsantsa. Amma fa jami'an leƙen asirin Amirka na gargaɗin cewar mai yiwuwa ne fa a tsakaninsu akwai dakarun ƙungiyar ta'adda ta Alƙa'ida da kuma na ƙungiyar Hizballah ta Shi'a.

Tababa akan matakan na soja

Kuma ganin yadda gaggan wakilan ƙasashen Larabawa da na Afirka suka ƙaurace wa zauren taron na London, abu ne dake nuna irin saɓanin dake akwai game da matakan na soja. Bugu da ƙari kuma ba wanda ya san tahaƙiƙanin halin da ake ciki a fagen yaƙin kuma akwai alamar komawar murna ciki dangane da fatan da aka yi cewar Ghaddafi zai tattra na sa ya na sa yai gaba idan ya fuskanci taron dangin. Gaba ɗaya dai ƙawancen na ƙasa da ƙasa ya shiga wani hali na gaba kura baya siyaƙi dangane da matakansa na soja kuma taron na London ya nuna cewar ba wanda ya san yadda zata kaya a game da rikicin na Libiya.

Mawallafi: Daniel Scheschkewitz/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar