Sharhi kan ziyarar da shugaba Bush ya kawo nan Jamus
July 14, 2006A lokacin ziyararsa a nan Jamus dai shugaba Bush ya sami kyakyawar tarbo da aka yi masa a garin Stralsund. Za a iya dai ganin bambancin wannan ziyarar da wadda ya taɓa kawowa a lokacin mulkin shugaba Schröder. A wannan lokacin dai, dangantaka ta yi sanyi tsakanin Jamus da Amirka. Amma yanzu, saƙon da shugaban na Amirka ke bayarwa shi ne, an sake farfaɗo da kyakyawar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Sai dai, duk mai lura da yadda shagulgulan tarbon shugaba suka kasance, zai ga cewa, kwaskwarima kawai aka yi. Ɗimbin yawan mutane kusan su dubu ɗaya, da suka taru suna yi ta cira wa shugaban hannu, wato zaɓansu aka yi. Su ko masu adawa da manufofin Amirka, waɗanda suka nemi yin zanga-zanga game da ziyarar, can wani wuri ’yan sanda suka keɓe su. Ko kusantar inda shugaba Bush ɗin yake ma, ba a bari sun yi ba. Babu shakka, shugaban bai san ma wasu sun yi zanga-zanga game da zuwansa nan Jamus ba.
A huskar siyasar ƙasashen biyu dai, za a iya cewa, an sami kusantar juna tsakanin Merkel da Bush, fiye da tsakaninsa da tsohon shugaba Gerhard Schröder. A da can Schröder ya fi cuɗanya ne da shugaba Putin na Rasha. Shi dai shugaba Bush ya bayyana matuƙar gamsuwarsa da irin kamun ludayin da Merkel ke yi a harkokin siyasar Jamus a halin yanzu.
A taron maneman labaran da shugabnnin biyu suka kira, Bush ya bayyana cewa, yana ba da muhimmanci ƙwarai ga ra’ayin da Merkel ke bayyana masa, a kan batutuwan da suka shafi harkokin siyasar ƙasa da ƙasa. Ya kuma ƙara da cewa, tana ɗaya daga cikin muhimman abokan burminsa a nahiyar Turai.
A ɗaya ɓangaren, Angela Merkel, za ta iya kambama kanta da nasarar da aka samu wajen kyautata hulɗa tsakanin Jamus da Amirka. Yanzu dai shugabannin biyu sun amince da juna, kuma ana kyautata zaton cewa, a kan duk wasu batutuwan da za su shafi harkokin siyasar ƙasa da ƙasa, Bush zai iya dogara kan Merkel wajen samun goyon baya, ba kamar a da lokacin Gerhard Schröder ba.
Sai kuma a ɗaya ɓangaren, wannan kusantar dai za ta iya dusashe duk wata sukar lamiri a kan wasu manufofin Amirkan, wadda a da can Jamus ba ta ɓata lokaci wajen bayyana ta.