Sharhi: Siriya- Ƙarshen yunƙurin diplomasiya?
August 3, 2012Domin Mr. Annan wanda ya taɓa samun kyautar zaman lafiya ta Nobel ya shiga cikin wani wadi na tsaka mai wuya a makonnin bayan nan. Duk da cewa ƙasashen yamma da China da Rasha da Iran da ma gwamnatin Siriya sun amince da shirinsa da ya tanadi ƙawo ƙarshen faɗan da neman hanyoyin warware rikicin cikin lumana, amma hakan ba ta samu ba, inji Dennis Stute a cikin wannan sharhin da Dennis Stute.
Shugaban mulkin kama karya na ƙasar Siriya Bashar al-Assad ya amince da sassautowa, amma a lokaci ɗaya ya ba wa dakarun tsaro umarnin ɗaukar ƙarin matakan ba sani ba sabo a kan 'yan tawaye da kuma fararen hula. Rasha da China sun yi ta hawa kujerar naƙi a Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya don hana zartas da ƙuduri kan Assad. Ƙasar Saudiya ta yi ta tura wa 'yan tawaye da makamai bisa sanin ƙasashen yamma. Ita kuma Turkiya ta buɗe ƙofofinta ga 'yan gudu hijira dake tserewa rikicin na Siriya. Sannan jami'an diplomasiya sun yi ta tsegunta wa 'yan jarida cewa Amirka ba ta yarda cewa shirin Kofi Annan na warware rikicin zai yi nasara ba. Tun da farkon fari 'yan tawayen Siriya sun yi watsi da shiga kowace irin tattaunawa da gwamnati.
Alamar rugujewar ƙoƙarin magance rikicin Siriya
Saboda haka murabus ɗin da Annan ya yi alama ce ta rugujewar duk wani yunƙurin magance rikicin cikin lumana. Yanzu haka ma da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa mutane dubu 16 sun rasu a rikicin yayin da dubun dubata suka yi ƙaura. Faɗan dai ya yaɗu zuwa sassan ƙasar daban daban.
Bayan rugujewar hanyoyin diplomasiya an fara ɗaga murya da kira da tsoma bakin soji. Kawo yanzu ƙasashen yamma na guje wa ɗaukar wannan mataki saboda abubuwan da aka gani a Afganistan da Iraƙi, ba za su so su shiga cikin wani yaƙi ba. Su ma ƙasashen ƙungiyar NATO ba sa duba yiwuwar ɗaukar matakai shigen na Libiya, wato kai farmaki ta sama a kan dakarun gwamnati, a ƙyale al'ummar ƙasa suna yaƙi suna kashe juna a ƙasa, abin da ke haddasa asarar fararen hula.
Dole za a dama da 'yan tawaye
Ko yaya dai 'yan tawayen ne za su tabbatar da makomar Siriya duk da cewa ba wanda zai iya sanin yadda hakan za ta kasance. Domin samun angizo a Siriya bayan Assad, ƙasashen yamma ba za su iya kawar da bukatar taimaka wa 'yan tawaye ba. Yanzu haka ma Amirka tana ba su fasahohi na dubarun yaƙi, sannan a fakaice tana tura musu da makamai. Hukumar leƙen asirinta wato CIA tana ƙasar Turkiya tana sa ido don hana makaman su shiga hannun ''yan ta'addar Al-Qaida. Duk da cewa gwamaiyar ƙasa da ƙasa ta hana tsoma bakin soji.
Dole ne a inganta hanyoyin kula da 'yan gudun hijira da suka warwatsu a ƙasashe maƙwabta da kuma fararen hula da faɗan ya rutsa da su a cikin ƙasar ta Siriya.
Mawallafa: Dennis Stute / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh