1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Taron G20 a Hamburg ya bar baya da kura

Engel Dagmar Kommentarbild App
Dagmar Engel
July 9, 2017

An so samun akasi a taron na kasashe masu ci gaban masana'antu burin dai ba na samun tashe-tsahen hankula ba ne ko da yake bai zamo mai muni ba, an samu rikici da lalata dukiya wanna kuwa sabon abu ne a dabi'ar Jamusawa.

https://p.dw.com/p/2gDxM
G20 Gipfel in Hamburg | Angela Merkel mit Polizisten
Angela Merkel, a tsakiyan 'yan sandan HamburgHoto: Reuters/J. Buettner

Wannan na daga cikin ra'ayin Dagmar Engel ta tashar DW, a cikin sharhin da ta rubuta bayan kammala taron na G20 a birnin Hamburg na Jamus. Tattaunawar ta kasashe 19 hadi da Kungiyar Tarayyar Turai ta so zama ba abin da ake muradi ba, kokari na samar da abin da kowa zai amince da shi a yayin taro bai zamo abu mai sauki ba, lamarin da ya haifar da gumin goshi, cikin mahalartan akwai masu fafutikar kare demokradiya na gaskiya da masu bin son zuciya a mulki da masu take hakkin bani Adama, wasu 'yan ba ruwana da masu tafe tsarinsu cike da cin hanci da rashawa sai kuma irinsu Trump masu tafiya da tsarin da ke kara dagula lamura na tafiya da cewa a komai "Amirka farko" 

Nasara

Karkashin wannan yanayi mutum zai iya cewa sakamakon taron kolin ya zama mai kyau, abin mamaki na zama yadda dukkanin mahalartan taro suka amince da watsi da akidar cinikayyar kayan cikin gida kawai, wanda ke ganin ba ayi masa adalci ba na da dama ta bibiyar dokokin kasuwanci na Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), abin da ke zama abin so ga Shugabar gwamnatin Jamus Merkel mai akidar a tafi tare da kowa.Tabbas wannan nasara ce da ke zama abin yabo ga shugaban kasar Faransa da takwaransa na Rasha.

Kommentarbild Kommentatorenfoto Dagmar Engel
Dagmar Engel Edita a DW

Ga batun sauyin yanayi kuwa a zahiri take sai an kalli tsari na siyasa da alkawuran kasashen kafin a bayyana nasara da aka cimma, Amirka dai ta tsame kanta daga yarjejeniyar ta Paris cikin yanayi mai jirwayen fari da baki, a karon farko a tarihin taron na G20 an samu masu barranta daga sauran mambobi, sauran kasashen 19 dai sun mara baya ga yarjejeniyar ta Paris, da abin ya yi muni kamar yadda mai rubuta sharhin ke fadi.

Kasawa

Amma ranaku kamar wadannan ba za su gamsar ba, akwai sabbin abubuwa kamar karfafa gwiwar mata da sabbin harkoki da za a kulla da kasashen Afirka, a kuma tabbatar da aiwatuwarsu da sabbin hanyoyin samar da ilimi duk wadannan ana bukatar lokaci. Taron na G20 har ila yau ya gaza wajen samar da sabuwar fiska da za a kalli tsarin duniya bai daya, a fadin duniya mutane sun amince tattalin arzikin duniya ba ya nufin jin dadin al'ummar duniya sai dai wasu daidaiku. A karshen taron dai Angela Merkel ta nuna rashin jin dadinta a dangane da masu zanga-zangar da da fari suka ce ta zaman lafiya ce sai dai ba a ga hakan ba. Wasu dai na zargin Merkel da kokarin amfani da taron da ke zuwa a shekarar da Jamus za ta yi zaben gama gari wajen nuna irin nasarar da ta cimma a idanun kasa da kasa.