1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Sudan a jaridun Jamus

Usman Shehu Usman RGB
June 8, 2019

Halin da ake ciki a Sudan da Talauci da ya addabi nahiyar Afirka da Siyasar Yuganda da kuma zargin cin hanci a Hukumar Kwallon KAfa ta Afirka CAF ne suka dauki hankulan jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/3K26Z
BG Sudan Proteste Sitzblockade vor dem Verteidigungsministerium in Khartoum
Hoto: Reuters/M. Nureldin Abdallah

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, Wacce ta yi labarinta bisa batun da ake rade-radinsa sai ga shi ya fara tabbata, wato cewar sojojin za su ja lokaci ne kawai, kafin su tasamma fararen hula. Kwatsam wasu gungun sojoji suka shiga tarwatsa maso boren daga sansaninsu, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 100 bayan jikkata wasu gwammai. A yanzu dai mazauna birnin Khartoum sun kasance tamkar wadanda aka yi wa daurin talala, domin basa iya fita da motocinsu cikin gari, bisa gudun farmakin sojoji na musamman da aka sani da RSF, wadanda aka  dorawa alhakin zubar da jinin da ya faru. Baya ga haka a ranar Litinin din da ta gabata, ko da a Laraba an sake harbe wasu  mutanen uku da suka fito sayen abinci a wani shago. Wannan dai lamari ne da duniya ta yi allah wadai da shi, to amma ga sojoji irin wannan allah wadai bai shiga kunnensu ba, domin ta kai sun soke duk tattaunawar da suka fara da fararen hula. 
 
Sai jaridar  Neue Zürcher Zeitung, wacce ta yi labarinta bisa tsananin talauci da a yanzu 'yan Afirka ke fama da su. Jaridar ta ce tsananin talauci dai yana daga cikin babbar matsalar al-ummar Afirka. A yanzu kashi 70 cikin dari na al'ummar suna rayuwa ne a kasa da dala daya a rana guda kamar yadda Bankin duniya ya wallafa. Inda jaridar ta ci gaba da cewa, dalilin hakan kuwa shi ne yayin da a kasashen Asiya ake kara samun raguwar talauci,  a kasashen Afirka kuwa matsalar sai karuwa take yi. Misali a Bara Kasar Najeriya ta wuce Indiya da yawan wadanda ke rayuwa cikin tsananin talauci. inda a yanzu aka yi kiyasi 'yan Najeriya kimanin miliyan 92, suna rayuwa ne cikin talauci, hakan kuwa ya nuna masu zama cikin talauci a zamanin gwamnatin Shugaba Buhari ya karu da yawan mutane miliyan goma in an kwatanta da shekaru uku baya. 


Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung,  ta duba siyasar kasar Yuganda ne, inda ta yi tsokaci bisa jajircewar da madugun adawan kasar Kizza Besigye ke yi na cewa zai sake karawa da Shugaba Museveni. Jaridar ta ce shin ana iya kada Museveni ta hanyar zabe? Shi kansu Kizza Besigye da aka masa wannan tambayar dariya ya yi ya ce sam, ba za iya kawar da Museveni kan mulki ta hanyar zabe ba. Dan shekaru 62 da haifuwa madugun 'yan adawan Yugunda, ya fi kowa sanin Museveni da harkar zabe, domin kuwa sau hudu suna karawa da juna, amma Yuweri Museveni na kada shi a zabe. Sai dai ayar tambayar ita ce shin ana yin zaben cikin 'yanci da adalci?  

Ugandas Oppositionsführer Kizza Besigye
Madugun adawar Yuganda, Kizza BesigyeHoto: DW/E. Lubega

Sai kuma batun cin hanci da harkar kwallon kafa. Inda jaridar die tageszeitung ta ce a lokacin da aka zabi Ahmad Ahmad a mukamin shugaban kungiyar kwallon kafan Afirka, kowa ya yi fatan ganin al'umara sun dai-daita, amma yanzu abin da ake ganin wata alama ce da ke sabanin hakan, wata kila ma mulkinsa ya zarta na wanda ya gada muni. Dan kasar Madagaska ya dare mulki a watan  Maris a shekara ta 2017 na shugabancin kungiyar kwallon kafan Afirka wato CAF,  bayan da samu nasarar kawar dan kasar Kamaru Issa Hayatou, wanda ya yi shekaru kusan talati yana jagorancin kungiyar bisa al-mubazzaranci.