1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar kisan Kim Jong Nam a Malesiya

Yusuf Bala Nayaya
October 2, 2017

Masu gabatar da kara a Malesiya sun bayyana cewa za a gabatar da shedu tsakanin 30 zuwa 40 a gaban kotu yayin da kwararu goma suma za su bayyana a shari'ar kisan dan uwan shugaban Koriya ta Arewa.

https://p.dw.com/p/2l587
Malaysia Kuala Lumpur Prozess wegen Tötung von Kim Jong Nam
Hoto: Getty Images/AFP/M. Rasfan

Mata biyu da ake tuhuma kan zargin kisan Kim Jong Nam dan uwan Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa, sun bayyana a gaban kotu a ranar Litinin din nan saii dai sun musanta zargin hannu a kisan.

Doan Thi Huong, 'yar shekaru 29, daga Vietnam, da Siti Aishah 'yar shekaru 25daga Indunusiya ana zargin sun shafa wani sanadari mai hadarin gaske a fuskar Kim, dan uwan shugaban na Koriya ta Arewa mai shekaru 45 a filin jiragen sama na  Kuala Lumpur a watan Fabrairu, ya kuma rasu ne sa'oi kadan bayan shafa masa wannan sinadari.

Masu gabatar da kara a Malesiya sun bayyana cewa za a gabatar da shedu tsakanin 30 zuwa 40 a gaban kotu yayin da kwararu goma suma za su bayyana. Idan har ta tabbata wadannan mata biyu na da hannu a kisan na Kim za su iya fuskantar hukuncin kisa.