Shari'ar laifukan yaƙi a Kenya
September 1, 2011Ministan ilmi na ƙasar Kenya, William Ruto wanda ake ganin zai tsaya takarar zaɓen shugaban ƙasar da zai gudana a shekara mai zuwa yau 01-09-2011 ake sauraron shari'ar da ake masa bisa zargin aikata laifukan yaƙi. Kotun hukunta miyagun laifuka ta ƙasa da ƙasa za ta yanke shawara akan ko shi da sauran jami'ai za su gurfanar a gaban kuliya bisa laifin hanzuga tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓen shekarar 2007.
Mutane kusan 1500 ne suka mutu a cikin faɗan da ya ɓarke bayan zaɓen da aka ta taƙaddama akai. Ruto da wasu abokan hulɗarsa biyu da ake zargi da aikata wannan laifi sun ba da goyon baya ga Raila Odinga da ya sha kayi a zaɓen kafin daga bisanin a bashi muƙamin fraimnista. A wannan watan ne kuma Uhuru Kenyatta wanda shi kuma ake ganin zai tsaya takarar zaɓen na shekara mai zuwa zai fuskanci shari'a.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Ɗanladi Aliyu