Shari'ar magudin zabe a Kenya
March 12, 2013Magoya bayan dan takarar adawa a zaben shugaban kasar Kenya Raila Odinga, sun gabatar da kukansu ga wata babbar kotun kasar, inda suke neman ta tilastawa hukumar zaben kasar da kuma kanfanin na'urar sadarawa ta Safaricom da su mika masa takardun bayanai domin karfafa zargin daya ke yi na cewar an sace kuri'u a lokacin zaben da Mr UHuru Kenyatta ya yi nasara.
Ya zuwa yanzu dai Odinga ya ki amincewa da nasarar da Kenyatta ya samu, amma ya bukaci magoya bayansa su kai zuciya nesa a dai dai lokacin da yake neman adalci daga kotunan kasar. Ya ce ya dauki matakin garzayawa kotun ne domin kaucewa maimaita rikicin daya biyo bayan zaben shugaban kasar Kenya a shekara ta 2007, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama.
Dama kuma kotun duniya da ke hukunta manyan laifukan yaki da ke da mazauni a birnin the Hague na kasar Holland, na tuhumar Kenyatta da hannu a rikicin na 2007.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou