Shawarwari kan rikicin nukiliyar Koriya ta arewa.
May 23, 2006Sakataren majalisar ɗinkin duniya Kofi Annan ya buƙaci rukunin ƙasashe shida dake shiga tsakani domin sasanta batun nukiliyar Koriya ta arewa da su gaggauta komawa teburin shawarwari don samun masalaha ta gano bakin zaren warware rikicin. Kofi Annan yace wajibi ne dukkan ɓangarorin su rubanya ƙoƙarin su domin sasanta taƙaddamar. Shawarwarin sulhunta rikicin nukiliyar ta Koriya ta arewa wanda ya kunshi kasashen China da Japan da Rasha da da Amurka da kuma Koriya ta arewa ya ci tura ne a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, bayan da Koriya ta arewan ta fusata da tsauraran matakan harkokin hada hadar kuɗaɗe da Amurka ta ɗauka a kan bankuna da kuma kamfanonin Koriya ta arewan bisa zargin musayar kuɗaɗen jabu da kuma wasu hada hada ba bisa kaída ba.