1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarwarin bude kan iyakar Kashmir da ta raba Pakistan da Indiya

October 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvNT

Makonni 3 bayan mummunar girgizar kasa a kudancin Asiya, Pakistan da Indiya sun fara shawarwari game da bude wani yanki na kan iyakar su ta Kashmir da ta raba kasashen biyu. An jiyo wakilan gwamnatocin kasashen biyu dake halartar taron a birnin Islamabad na cewa an amince da wasu dokoki wadanda zasu ba dangi da iyalai da ke zaune a bangarorin dake daura da juna na wannan kan iyakar damar taimakawa juna ba da wata tsangwama ba. Yayin da Pakistan ta ba da shawarar bude kan iyakoki biyar, Indiya cewa ta yi zata kafa cibiyoyi 3 a yankin ta na Kashmir don ba da agaji ga masu fama da bala´in girgizar kasar. Akalla mutane dubu 55 suka mutu sannan miliyoyi suka yi asarar gidajensu sakamakon mummunar girgizar kasar da ta auku a ranar 8 ga wannan wata na oktoba.