Sheikh Ahmed na Somalia ya yi saranda a Kenya
January 22, 2007Talla
Daya daga cikin shugabannin kotunan Islama na Somalia ya mika kansa ga hukumomin Kenya da na Amirka, kuma yanzu haka ana tare da shi a birnin Nairobi. Sheikh Sharif Sheikh Ahmed wanda wani jami´in diplomasiyan Amirka ya bayyana shi da cewa mai sassaucin ra´ayi ne kuma zai iya taka rawa wajen sassanta bangarorin dake fada da juna a Somalia, ya tsallake zuwa Kenya kuma nan take aka kai shi Nairobi. A kuma can birnin Mogadishu ana ci-gaba da musayar wuta tsakanin sojojin sa kai da dakarun Ethiopia. A kuma halin da ake ciki kasar Malawi ta bi sahun Uganda wajen nuna aniyarta ta ba da gudunmmawar dakaru ga rundunar kiyaye zaman lafiya da kungiyar tarayyar Afirka zata girke a Somalia. Da farko Ethiopia ta ce ba zata janye sojojin ta daga Somalia ba har sai rundunar kungiyar ta AU ta isa can.