1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da hari mafi muni a Pakistan

Yusuf BalaDecember 16, 2015

Wannan hari dai ya gurgiza kasar da ma al'ummar duniya koda yake kasar ta kwashe gwamman shekaru tana ganin irin wannan tashin hankali.

https://p.dw.com/p/1HNzh
Pakistan erster Jahrestag nach dem Terrorangriff auf die Schule in Peschawar
Hoto: privat

Mahukunta a kasar Pakistan sun baza jami'an tsaro da 'yan sanda a manyan birane da ke kasar yayin da a ranar Larabar nan ake tunawa da cika shekarar daya da kisan gillar da kungiyar Taliban ta yi wa yara 'yan makaranta a wani mummunan hari da yayin sanadi na rayukan mutane 151. Wannan hari dai ya girgiza kasar da ma al'ummar duniya koda yake kasar ta kwashe gwamman shekaru tana ganin irin wannan tashin hankali.

Harin da aka kai a wannan makaranta da ke karkashin jami'an soji a garin Peshawar da ke Arewa maso Yammaci da ya yi sanadin rayukan mafi akasari kananan yara na zama mafi muni da mayakan suka kai, abin da kuma a fadar Akbar Khan da ke wakiltar iyayen yara 124 da aka raunata yaransu ke cewa har yanzu harin na taba rayuwarsu.

"Ilimin yaran an tsaida shi, wasu an mai da su guragu, dole a dauki lokaci ana basu kulawa musamman abin da ya shafi kwakwalwa ba su kadai ba har ma da iyayensu".

Ana sa rai dai Firaminsta Nawaz Sharif da wasu manyan jami'an shugaban rundinar soji Raheel Sharif da jagoran 'yan adawa Imran Khan za su halarci bikin a wannan makarantar soji a birnin na Peshawar.