Nijar: Shekaru 10 da hambarar da mulkin Tandja
February 18, 2020A ranar hudu ga watan Agusta na shekarar 2010 ne tsohon Shugaban Kasa Tandja Mamadou ya shirya zaben raba gardama domin samar da wani sabon kundin tsarin mulki da zummar kawo karshen cece-kuce da ya barke a lokacin mulkinsa kan neman karin wani wa’adin mulki na tsawon shekaru uku bayan ya shafe tsawon shekaru 10 yana jan ragamar iko.
Sauya kundin tsarin mulkin da ya bai wa Shugaba Tandja damar zarcewa ya bar baya da kura, hayaniya ta barke tsakanin bangarorin siyasar kasar Nijar masu da’awa da matakin shugaban da kuma masu nuna tsananin kyama game da hakan, kana kuma rarrabuwar kawunan jama’a ta tsananta inda har aka kai ba’a ga maciji a tsakanin masu nuna kauna da kuma masu adawa da gwamnatinsa.
A ranar 18 ga watan Febrairu rundunar sojan Nijar karkashin jagorancin Kwamanda Salou Djibo ta hambarar da mulkin Shugaba Tandja tare da rusa sabon kundin tsarin mulkin da ya bai wa Shugaba Tandja damar tsawaita wa’adin mulki, sun kuma rusa duk wasu hukumomin da ke karkashin tsohuwar gwamnatin ta farar hula tare da kafa wata sabuwar hukuma ta rikon kwarya mai suna CNRD wacce ke da burin sake mayar da turba ta dimukuradiyya a Nijar.
Murna da hambarar da mulkin Tandja Jama'a sun fito domin nuna murna da yadda sojojin suka hambarar da mulkin na tsohon shugaban kasar Tandja, tare da nuna goyon bayansu ga matakin da sojojin kasar suka dauka na kifar da gwamnatin farar hula wadda suke zargi da karya tafarkin dimukuradiyya. Sowa da murna da farin ciki sun mamaye fuskokin mazauna birnin Yamai kwanaki biyu kuma sun tabbatar da hakan a yayin wata zanga-zangar da suka fito kan tituna inda suka bayyana cewa sun gamsu da matakin soja.
Sai dai shekaru 10 bayan hambarar da mulkinsa har yanzu wasu na yi wa hambararen tsohon shugaban kasar kallon wani jarumi da bai yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa ba, tare da kare yan kasar. Ya kuma yi jan kokari wajen kare hakin talaka da bai wa mai karamin karfi kulawa ta fannin kiwon lafiya da ilimi da wasu fannonin na dabam da jama‘a suke bukata.
Ci gaba ko akasin haka a yayin mulkin Tandja Masu sharhi kan al'amurran siyasa na ganin an samu ci gaba fiye da yadda ake zato a yayin mulkin Tandja. Sai dai wasu na kallon an samu koma baya a tafarkin dimukuradiyya duba da kudrin shugaban na sauya kundin tsarin mulki, baya ga wasu hanyoyin na dabam da suka kara muzanta kasar ta fannin siyasar tattalin arziki, inda fatara da rashin aiki suka gagari magancewa daga gwamnatin duk da kokarin da wasu ke ganin gwamnatin ta yi a wannan lokaci.
Duk da hambarar da shi kan madafan iko, Shugaba Tandja ya hako man fetur a Diffa sannan ya samar da matatar man fetur a yankin Damagaram, matsayin babban tubali na tattalin arziki da gwamnatin mulkin soja ta gada. Ya kafa tubalin samar da madatsar ruwa ta Kandadji a yankin Tillaberi, ya kudiri aniyar samar da tashar dakon kaya ta tudu a yankin Dosso, baya ga wasu muhimman ayyuka na ci gaban karkara a yankunan kasar da dama ciki har da Tahoua da yankin Agadez mai tarihi.
A yanzu tsohon shugaban kasar kuma tsohon hafsan soja da ya rikide ya koma siyasa Tandja Mamadou na da shekaru fiye da 80, yana zaune a wani gidansa da ke dab da shigowa Yamai babban birnin kasar. Yana kuma samun ziyarar jama'a akai-akai musamman ma magoya bayansa da wadanda suka yi masa fatan ganin ya dore a kan madafan iko.