1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Idriss Deby: Shekaru 30 a kan mulkin kasar Chadi

Abdoulrazak Garba Babani MNA
December 1, 2020

Shekaru 30 ke nan da kungiyar 'yan tawayen MPS karkashin jagoranci Idriss Deby Itno ta shiga birnin Ndjamena ta kwace mulkin kasa daga shugaba Hissene Habre.

https://p.dw.com/p/3m5SX
Tschad Präsident Idriss Deby Itno
Hoto: DW/B. Dariustone

A ranar 1 ga watan Disamban shekara ta 1990 kungiyar 'yan tawayen MPS karkashin jagorancin shugaban Chadi Idriss Deby Itno ta kutsa birnin Ndjamena ta kwace mulkin kasa daga shugaba Hissene Habre. Daga bisani kungiyar ta MPS ta rikide ta koma jam'iyyar siyasa, wadda a karkashinta Shugaba Deby yake shugabancin kasar ta Chadi.

Tun daga wancan lokaci a duk zabe shugaba Idriss Deby Itno ke lashe zaben da ake gudanarwa a kasar a tsawon shekaru 30 na mulkinsa, duk da irin korafi da 'yan adawa ke yi da kiran manyan kasashen duniya su zuba ido su gani ba dimukuradiyya ake yi a Chadi.

Karo na biyar kuma a zaben da yake ikirari na dimukuradiyya ne, yana yin nasarar lashe zabe a matsayin shugaban kasa dan farar hula.

Karin bayani: Chadi: Shekaru 60 na 'yanci daga Faransa

Kuma shekaru biyu da ya gabata an sabunta kundin tsarin mulkin kasar, saboda haka shugaba Idriss Deby ya sake samun damar sake tsayawa neman shugabancin kasa a wani sabon zagaye na sabon kundin mulkin kasa a karo na farko maimakon a karo na shida. 

Dan adawar kasar Chadi Succès Masra
Dan adawar kasar Chadi Succès MasraHoto: Blaise Dairustione/DW

Ra'ayoyin jama'a sun bambanta game da wannan hali na tsawon shekaru 30 da kasar ta Chadi ta kwashe karkashin shugaba daya tilo.

Umar Adamu Waziri tsohon dan siyasa da aka yi da shi jiya ake kuma damawa da shi yanzu ya ce "a siyasar kasar Chadi babu ci-gaba wato ba a yi baya ba kuma ba a ci-gaba ba, idan aka duba shekaru 30 na tsawon mulkin Idriss Deby. Sai dai an dan samu 'yancin fadin albarkacin baki ba kamar sauran gwamnatocin da suka gabata ba." 

A yayin da Hamza Umar Babban sakataren kungiyar Asusu ta Hausawan Chadi ya ce idan aka dubi tsawon shekaru 30 na mulkin jam'iyyar MPS, to "a iya cewa babu ci-gaba kwata kwata babu a fagen ilimi, babu a kiwon lafiya, babu a harkokin tattalin arzikin talakawan kasar. Sai dai an samu ci-gaba a fannin tsaro."