Shekaru 30 da zanga-zangar da ta kawo karshen Jamus ta Gabas
October 9, 2019A ranar 9 ga watan Oktoban 1989 mutane kimanin dubu 70 suka gudanar da wata zanga-zangar neman 'yancin walwala da tsarin mulki na dimukuradiyya a birnin Leipzig. Wannan zanga-zangar ta yi wajen kifar da gwamnatin Jamus ta Gabas.
Da yammacin ranar 9 ga watan Oktoban mutane fiye da dubu 70 daga dukkan bangarori na al'ummar Jamus ta Gabas suka fantsama kan tituna don nuna fushinsu ga gwamnatin kwaminisanci, duk da cewa an haramta irin wannan gangami. Mafi yawa daga cikin masu zanga-zanga sun yi tsammanin 'yan sanda za su farma musu, kasancewa an girke dakaru cikin motoci masu sulke a birnin, musamman da yake zanga-zangar ta zo ne kimanin watanni hudu bayan murkushe wani bore a dandalin Tian'anmen na kasar China.
Sai dai abin mamaki hukumomi sun kyale masu zanga-zangar yin jerin gwano a tsakiyar birnin na Leipzig suna kira da a ba su 'yancin walwala da shirya zabe na gaskiya ba tare da tashin hankali ba.
Shekaru 30 ke nan. Kathrin Mahler Walter da a lokaci take matashiya 'yar shekaru 18 ta kasance a cikin masu fafatukar kare 'yancin al'umma wadda tace ranar tsoro ya fita zukatan mutane.
A 1989 gwamnatin Jamus ta Gabas da a lokacin ta cika shekarun 40 da kafuwa ta tsinci kanta cikin matsalolin siyasa da na tattalin arziki. Mutane na yin kokarin tserewa kungiyoyin fafatuka kuma na kara samun goyon baya. A lokacin ne kuma Mikhail Gorbachev ya fara aiwatar da sauye-sauye a Tarayyar Sobiet kuma kasashen gabaci irin su Poland da Hungary suka fara bude kofofinsu, to sai dai mahukuntan Jamus ta Gabas karkashin tsohon Shugaba Erich Honecker sun ki duk wasu sauye-sauye.
Tashar telebijin ta Jamus ta Gabas ba ta ba da labarin zanga-zangar, to amma bisa jajircewar wasu 'yan jarida masu daukar hoto cikin har da Siegbert Schefke duniya ta samu labarin abubuwan zanga-zangar ta ranar 9 ga watan Oktoba, inda a boye ya tura wa 'yan jarida na yammaci fina-finan bidiyon da ya dauka.
Wai me yasa 'yan sanda da sojoji ba su yi harbi a kan masu zanga-zangar a ranar 9 ga watan Oktoba a birnin na Leipzig ba, sabanin yadda ya faru a Berlin a 1953 ko a Beijing a watan Maris na 1989? Masu zanga-zangar sun bi hanyoyin ba tare da sun tunkari jami'an tsaro ba.
Wata daya bayan zanga-zangar ta birnin Leipzig, katangar Berlin ta fadi wato 9 ga watan Nuwamban 1989, ranar da ke da muhimmanci da kusan duk Jamusawa, to amma kadan daga ciki musamman matasa suka san abin da ya faru a Leipzig wata daya gabaninsa. Sai dai zanga-zangar ta lumana ta shiga tarihin a matsayin juyi- juya hali na lumana na farko a Jamus.