1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru uku da dawowar Taliban kan mulki

Abdullahi Tanko Bala
August 14, 2024

Shugabannin Taliban a Afghanistan sun yi bikin cika shekaru uku da dawowa karagar mulki

https://p.dw.com/p/4jSs2
Amir Khan Muttaqi ministan harkokin wajen Afghanistan
Amir Khan Muttaqi ministan harkokin wajen AfghanistanHoto: Yegor Aleyev/TASS/IMAGO

'Yan Taliban sun yi bikin cika shekaru uku da dawowa karagar mulki. Bikin ya gudana a tsohon sansanin sojin sama na Amurka da ke Bagram a Afghanistan, sai dai babu wani bayani game da wahalar da ake sha a kasar ko kuma alkawurar samun kyakkyawar fata ga 'yan kasar da ke fadi tashi.

Daruruwan jama'a ciki har da jakadun kasashen China da Iran suka halarci bikin da aka gabatar da jawabai da kuma faretin soji.

A ranar 15 ga watan Augustan 2021 ne mayakan Taliban suka kwace birnin Kabul bayan da gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan Amurka ta rushe kuma shugabanninta suka tsere.