1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Masu adawa da sojoji na shiga gwamnati

Salissou Boukari SB/ZUD
March 6, 2024

Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta yi nade-nade da ake gani 'yan siyasa daga bangaren tsohuwar gwamnatin da aka kifar suna shiga gwamnatin sojojin.

https://p.dw.com/p/4dEWK
Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar Nijar
Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

A Jamhuriyar Nijar wani sabon cece-kuce ne ya kunno kai tun bayan da a taron majalisar ministoci na baya-bayan nan aka yi wasu sabin nade-nade wanda ake ganin tamkar mambobin jam'iyyar PNDS Tarayya ce da aka hambare suke dawowa sannu a hankali lamarin da ya harzuka zukatan wasu 'yan kasar, sai dai kuma a hannu daya wasu 'yan kasar na ganin cewa ya kamata a yi hattara don kar a koma mulki na wariya kaman yadda 'yan siyasa suka yi a baya. 

Karin Bayani: Nijar: Ba ta sauya ba a kan iyakokin kasar

Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine na Jamhuriyar Nijar
Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine na Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou/DW

Tun dai da jimawa sakamakon nade-nade da aka yi ta yi a cikin wannan sabuwar tafiya ta mulkin soja mutane sun yi ta yin korafi kan kasancewar wasu da aka bai wa mukamai a wannan sabuwar gwamnati, inda ake danganta su da tsohuwar gwamnatin da aka yi wa juyin mulki sakamakon rashin iya gudanar da kyaukyawan mulkinta kaman yadda sojojin suka zarge ta. Sai dai kuma bada mukami na baya-bayan nan ya sake tayar da tsohon balli inda masufafutukar ganin an samu sauyi ke ganin cewa ana son komawa gidan jiya Noman Goge. Oumarou Souley, shugaban kungiyar farar hula ne na FCR da ke fafutikar kare hakin jama'a ya ce su abin bai ba su mamaki ba.

A fuskar 'yan siyasa musamman na bangaran gwamnatin da aka kifar ta tsohon Shugaba Bazoum Mohamed, ta bakin Sahanoune Mahamadou ya ce sannu a hankali mutane za su gane gaskiyar lamarin abin da suke yin suka a kan shi.

Masu goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Masu goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

A bangaren kungiyar da ke fafutikar yaki da cin hanci da rashawa da gudanar da kyaukyawan mulki ta bakin shugabanta Omar Adamou na ganin cewa ya kyautu fa mutane su rika sara suna duba bakin gatari. Sai dai kuma A dayan bangaran shugaban kungiyar ta Stop corruption Omar Adamou ya yi kira ga magabata da su saka idanu kan ma'aikatan da ke hana ruwa gudu a cikin ma'aikatu daban-daban na gwamnati :

Baya ma ga wannan matsala ta bayar da mukamai da ke haifar da cece-kuce, akwai kuma shi kansa batun yaki da almundahana da dukiyar kasa da ake yi, inda wasu 'yan kasar ke zargin cewa ana karbar kudade daga hannun wadanda aka zarga da handama amma daga bisani ana sallamarsu ba tare da sun fuskanci kuliya ba, lamarin da wasu kuma ke ganin cewa fitowa ana ba da bayani lokaci zuwa lokaci ga 'yan kasa shi ne ke magance cece-kuce tsakanin al'umma.