1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin China kawa ce ta hakika ga Afirka?

August 17, 2012

Rawar da nahiyar Afirka ta taka a wasannin Olympics da aka kammala a London ranar Lahadi, yana daga cikin al'amuran da jaridun Jamus suka duba a wannan mako game da nahiyar.

https://p.dw.com/p/15rnd
Hoto: dapd

Jaridar Neue Zürcher Zeitung alal misali, tace Kenya bata sami yadda taso ba a wasannin na Olympics, inda ma jami'an wasanni da wakilan gwamnatin kasar suka azurta kansu daga kudaden da aka ware domin horad da yan wasa. Abin da ya zama sakamakon hakan kuwa shine rashin samun lambobi masu yawa a wasannin na bana. Maimakon lambobin zinariya shidda da Kenya din ta koma gida dasu daga wasannin da aka yi shekaru hudu da suka wuce a Peking, a bana yan wasan ta lambobin zinariya biyu kawai suka samu. Jaridar tace maimakon nuna bakin cikin wannan koma-baya, sai gashi dimbin magoya baya sun hallara a tashar jiragen sama domin yiwa yan wasan murnar kwarya-kwaryar nasarar da suka samu. Matsalar yan wasan Kenya, kamar yadda jaridar Neue Zürcher Zeitung take gani, ta sami asalin ta ne tun ma kafin a bude bikin na birnin London. Yayin da Kipchoge Keino, shugaban kwamitin Olympics na Kenya yaso yan wasan a tura su Bristol a Ingila domin samun horo, mataimakin sa ya nuna yafi son su zauna kamar yadda suka saba su sami horon su a gida. Irin yadda banbanci tsakanin jami'an wasanni da wakilan gwmanati yakan shafi matsayin wasanni a Afirka, ana iya ganin sa ba ma a Kenya kadai ba, amma a nahiyar Afirka baki daya, idan aka y inazarin irin rawar da suka taka a wasannin na Olympics a bana.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi sharhi a game da halin da ake ciki na ko-ta-kwana a wuraren hakar ma'adinin Platinum a Afirka ta kudu. Yajin aikin da ya faro a matsayin na neman karin albashi a Afirka ta kudun, ya kai ga dauki ba dadi tsakanin ma'aikatan hakar ma'dinin da jami'an tsaro, tare da zub da jini. Yanzu kuma wannan rikici yana barazanar yaduwa zuwa sauran wuraren hakar wasu ma'adinai a kasar. Jaridar tace wannan rikici na ma'aikata yana samuwa ne a daidai lokacin da masana'antun hakar Platinum na Afrika ta kudu suke fama da asarar ciniki a kasuwannin duniya.

Jaridar Berliner Zeitung ta duba batun kara angizon kasar China a nahiyar Afirka, tare da tunatar da cewar komai yayi yawa ya baci, wanda saboda haka ne a Afirka din ake kara samun masu daga murya suna nuna adawa da Chinan na mamaye dukkain hanyoyin zuba jari a wannan nahiya. Jaridar tace China dai tana nuna kanta ne a matsayin kawar nahiyar Afrika, to amma ana samun karuwar mutanen dake dari-dari da kasancewar ta a yankin, musamman idan aka lura da karuwar zanga-zanga a kamfanoni ko wuraren da Chinan take da angizo a cikin su. Rikicin baya bayan nan tsakanin yan Afirka da yan kasuwa ko injiniyoyi ko ma'aikatan China, ya faru ne a wani wurin hakar kwal mallakin China a Zambia, inda a makon jiya, ma'aikata cikin fushi suka kashe wani manaja daya dan China, suka kuma jiwa wani rauni. A kasar Zimbabwe ma, ma'aikata tuni suke korafi game da ma'aikata yan China, haka nan a Afirka ta kudu da sauran kasashen nahiyar inda kamfanoni maIlakar China suka sami gindin zama.

Arbeitskampf in südafrikanischer Mine Marikana
Zanga-zangar ma'aikatan ma'adinin Platinum a Afirka Ta KuduHoto: Reuters

Tare da wannan sharhi na jaridar Berliner Zeitung game da adawar yan Afirka kan angizon China a nahiyarsu zamu dakata.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Usman Shehu Usman