Shin ko Afirka ta samu nata 'yan Taliban
July 3, 2012Wanna wani saƙone mai birkitarwa: Inda a aka samu labarin cewa yan tawaye masu kaifin kishin Islama sun ruguza ɗaukacin hubbare dake birni Timbuktu. Saƙon mai birkitarwane sabo da bawai kayan tarihin birnin kadai aka rusa ba, amma tarihin nahiryar ce baki daya. Wannan hujja ce mai ƙarfi da yakamata ƙasashen duniya su dauka na yaƙar hatsarin yan ta'adda. Babbar Editar tashar DW Ute Schaeffer ta rubata sharhi a kai.
Wata alamace ta yin gargadi, inda Yan tsagerun na ƙungiyar Ansar Din suka yi amfani da diga da wuta wajen rusa hobberen waliyan da aka tinƙaho da su a birnin Timbuktu. Gargaɗin ba mai wani ƙarfi ba, kuma an nufe shi ne da ƙasashen yamma, amma kuwa zai tasiri kan tarihi da al'adun yankin, kamar yadda duniya ta son Timbuktu a matsayin ƙasar da ke da soraye tun daduruwan shekaru. Bayan kammala ɗanyan aikin nasu wani mai iƙararin shine kakakin ƙungiyar, Sanda ul Boumana yace sun gama ruguza hubbare 16 na waliye da kuma wadan ke a manyan masallatai uku na birni mai ɗaɗɗen tarihi wato timbuktu, daga nan tsagran sai yayi kabbara.
Kamar a Afganistan
Tun shekara ta 1988 birnin Timbuktu ya kasance a jirin biranen duniya na tari dake ƙarƙashin hukumar kula da al'adu ta MDD wato UNESCO. Kana tun a makwanni wannan hukumar ta UNESCO ta fara yin gargadi bisa hatsarin da kayan tarhi a Timbuktu ke fiskanta. Su dai wadanna yan tawaye Abzinawa dake kaifin kishin Islama daka sani da Ansaru Din abinda suka aikata dai yake da wanda ƙunguiyar Taliban ta yi a Afganistan, wadanda suka rusa wani wurin Ibadan Budda, halayen iri dayane, aƙidodjin dayane kuma yadda aka yi rushe rushen ɗayane.
Bayan da sojin Amirka suka mamaye Afganistan suka fara farautar yan Alƙa'ida, sannu a hankali yan ƙungiyar suka fara ƙaura izuwa yakin Sahel. ƙungiyoyin biyu da suka fara aikin ta'andancin tun shekaru masu yawa, sun kafu a waɗannan nahiyoyi dake da aksarin jama'arsu musulmai ne. Kai a yanzu mutun zai iya cewa sun mamaye duniya baki ɗaya.
Alƙa'ida ta kafu a Afirka
A ƙasar Yamen da da ƙasashen Sahel, Alka'ida na iya laɓewa tana horar da mabiyanta. Daga nanan ake ƙinƙeshe sojojin ƙungiyar kana a aikasu sauran sassa na nahiyar. Wannan matkin wata dabare ce ta rikita nahiyar Afirka baki daya. Lamrin ya aurayane, da gwamnatocin mafa ƙarfin iko, da ƙungiyoyi masu aikata laifi da kuma, da rashin cibiyoyi masu ƙarfi, kana uwa uba tsagerun ƙungiyoyin dake da kaifin kishin Islama. Wadannan sune suka haifar da Alƙa'ida a Afirka. Dahaka suka kafa wata jinka wanda ta kaiga wurare irinsu Arewacin Najeriya. Annan yanzu ƙungiyoyin yan ta'adda dake Turai suna komawa Afirka.
Rikicin addini a Najeriya
Tun lokacin da aka fahimci irin wannan hada kai da, tsakanin kungiyoyin babu wanda zai rane ƙarfin da suke da shi. Ƙungiyar Boko Haram a Najeriyata sha daukar alhakin kai hare hare mujami'in ƙasar, tun jimawa aka fara cewa wannan ba danyen aiki yan ƙasa bane kawai, don haka wasu ke ganin cewa suna samun tallafi daga waje. Ita dai ƙungiyar Alƙa'ida ana zaton cewa tana samun kudinta daga fansar sace mutane, da sayar da muggan ƙwayoyi da kuma safarar makamai, kudin da take samu daga wadannan hanyoyin tana rabawa ƙungiyoyi dake ƙarƙashinta a fadin duniya.
Lamarin ya fi ƙarfi mahukuntan yankin
Dole ƙasashen Turai da Amirka su fito a fili. Sojan ƙasar Mali su kadai ba za su iya yaƙar yan tawaye da mayaƙan Islama dake arewacin ƙasar ba. Suma ƙasashe maƙobta da Mali ba za su iya kawar da yan ta'adda a ƙasar ba. Misali Mauriteniya dake iyaka da Mali ta yamma ta sha fama da juyin Mulkin soji, haka ita Jamhuriyar Nijar da ke iyaka da Mali ta gashi, gwamantocin ƙasashen basu basu jima kan mulki da za su iya yin wani abun azo a gani. Don haka mafita itace, matakin ƙasar Amirka da Faransa wanda ta rani Mali, wannan shine kada ya saura, dole Turai duk da rikicin kudi da take fama da shi, amma ta yi hobbasa don kawo ƙarshen rikicin Mali.
Mawallafa: Ute Schaeffer / Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu