1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin Paul Biya ne tushen rikicin Kamaru?

Binta Aliyu Zurmi
August 31, 2018

Kimanin wata guda gabanin gudanar da babban zabe a kasar Kamaru, rikici tsakanin sojoji da 'yan a ware a yankunan da ke amfani da harshen Ingilishi na kara karuwa.

https://p.dw.com/p/347QC
Kamerun Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya Hoto: picture alliance/abaca/E. Blondet

Shugaba Paul Biya ya kasance mai mulkin kasar Kamaru tsawon shekaru 36 kuma har yanzu ba shi da niyyar sauka daga karagar mulki duk da cewa shekarunsa sun ja, domin yana da shekaru 85 da haihuwa. 'Yan Kamaru da ke zaune a Jamus suna damuwa game da abin da ke faruwa a kasarsu tare da fatan za a gudanar da zabe lami lafiya. Wannan dalilin ne yasa sukan hadu duk shekara don tatauna mafita.

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Wasu 'yan Kamaru a yankin IngilishiHoto: Getty Images/AFP

Wasu ‘yan Kamaru mazauna birnin Bonn na Jamus kan yi taro domin samun labarai akan rikicin da ke ci gaba da gudana a gida a bangaren kasar da ake magana da turancin Ingilishi. Kungiyar ta kunshi bangarorin biyu na 'yan a ware da kuma gwamnati. A gefe guda kuma mata ne ke gyara kifi da nama da mazan zasu gasa.

A tukubar gasa naman, sun ci gaba da tatauna batutuwan akan damuwarsu game da tashin hankali a gida da kuma sukar jagorancin Shugaba Paul Biya. Masu amfani da Turancin Ingilishi da masu amfani da harshen Faransanci duk suna korafi akan mulkin Shugaba Biya. Jean Paul Brice Affana dan Kamaru ne mazaunin Bonn kuma mai rajin kare muhalli.

"Ya kasance a kan karagar mulki ne domin son kai na mutanen da ke kusa da shi wadanda ke neman kare muradunsu"

Jeffrey Smith, babban darakta ne a kungiyar Vanguard Afrika, kungiyar da ke ba da goyon baya ga zaben gaskiya da adalci a Afirka. Ya dora laifin rikicin da ke faruwa a Kamaru akan shugaban kasar Paul Biya.

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Jam'ian tsaro a yankin Ingilishi na KamaruHoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

"A halin da ake ciki, rikice-rikicen da Kamaru ke fama da su a yanzu duk sun samu ne sanadiyar Shugaban Paul Biya. Paul Biya ya kasancee shugaba mai mulkin kama karya na Afirka"

Ba kamar gida ba, 'yan Kamaru da ke zaune a Jamus suna da kyakyawar alaka a tsakaninsu kuma suna fatan ganin chanjin a kasarsu, kamar yadda Tambi Tabong likita wanda shi ke shugabancin kungiyar 'yan Kamaru a birnin Bonn ya bayyana.

"Mun dade muna adduar fatan ganin chanji. Duk wani mai tunani na da burin ganin an sami chanji a Kamaru"

An zuba ido a ga yadda Shugaba Paul Biya na Kamaru zai magance matsalolin da ke fuskantar kasarsa, ciki har da rikicin da ya shafi akalla mutane miliyan biyar. 'Yan takara takwas ne za su kalubalanci Paul Biya a zaben shugaban kasda da zai gudana a ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa. Sai dai rashin hadin kai tsakanin 'yan takarar adawa na haifar da nakasu ga wannan buri nasu.