1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunanin 'yan Afirka kan yiwuwar dawowar Trump

Martina Schwikowski AT Bala/SB
February 7, 2024

Yiwuwar dawowar Trump fadar White House bayan zaben da za a yi a Amurka ya fara damun wasu 'yan Afirka musamman a game da manufofinsa kan 'yan gudun hijira da 'yan cirani da kuma rashin ba da hadin hadin kai ga nahiyar.

https://p.dw.com/p/4c8gM
Amerika: Magoya bayan Donald Trump kan zaben 2024 a New Hampshire
Magoya bayan Donald TrumpHoto: Brandon Bell/AFP

 

Tsohon shugaban na Amurka Donald Trump ya kasance dan takarar da ke gaba da zai yi wa Jam'iyyar Republican takara a zaben shugaban kasar Amurka da zai gudana a watan Nuwambar 2024. A Afirka ra'ayoyi sun sha bamban a kan yadda suke kallon dawowar ta sa. A kasar Ghana alal misali, ra'ayoyin jama'a a Accra babban birnin kasar sun bambanta a kan wanda suke gani ya fi cancanta tsakanin Trump da shugaban kasar Joe Biden.

Karin Bayani: Trump ya zama dan takarar shugaban kasa a lowa

Donald Trump lokacin yakin neman zabe
Donald TrumpHoto: Pablo Martinez Monsivais/AP Photo/picture alliance

Wata daliba a Ghana Abigail Grift ta ce ko kusa ba ta son ganin Trump ya samu wani wa'adin mulki, ta shaida wa DW cewa Shugaban kasa Joe Biden shi ya cancanta da wannan mukami bayan da aka samu Trump da laifin yi wa wata marubuciya E. Jean Carooll kazafi.

A daya bangaren kuma Samuel Osofo, ya ce zai yi matukar farin ciki idan aka sake zabar Trump, saboda hangen nesa wajen taimakon kasashen Afirka. Etse Sikanku, malami a Jami'ar koyar da aikin Jarida da harkokin sadarwa da ke birnin Accra fadar gwamnatin Ghana ya shaida wa DW cewa akwai bukatar Afirka na da dalilai ta nuna damuwa kan yiwuwar Donald Trump ya sake dawowa kan karagar mulki. saboda irin akidar da ke jan ramagar ayyukansa. Sikanku ya yi nuni da rahotanni  da aka yi ta yadawa a 2018 na kalaman kaskanci da Trump ya yi amfani da su baiyana wasu yan sassan Afirka yayin da yake nuna adawa da yan cirani daga wadannan kasashe.

Siyasar Amirka
Siyasar AmirkaHoto: DW

Ga wani manazarci dan kasar Afirka ta Kudu Daniel Silke, abin la'akari shi ne manufa a dangantakar kasa da kasa. Gwamnatin Biden tana kokarin fadada tasirinta a Afirka da karfafa dangantakar diflomasiyya  da kasashen Afirka. Wannan manufa za ta ci gaba ko Biden ko Trump ko ma waye yake mulki. Sai dai kumaSilke ya ce duk da hargowar da Trump ya ke yi na Amerca First cewa Amurka ce farko a duk abin da ya sanya a gaba, duniya na bukatar azama daga Amurka. Karin karfin da China da Rasha da sauran kasashe suke yi za su tilasta gwamnatin Trump zaman saniyar ware fiye da yadda ba a tsammani.