1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin amfani da karfin soja kan Koriya ta Arewa

Gazali Abdou Tasawa
July 29, 2017

Amirka da Koriya ta Kudu sun sanar da soma nazarin daukar matakan soja kan Koriya ta Arewa domin taka mata birki a game da shirinta na nukiliya biyo bayan sabon gwajin makami mai linzami da ta gudanar a ranar Jumma'a. 

https://p.dw.com/p/2hL8R
Nordkorea Raketentest Hwasong-14
Hoto: Getty Images/AFP/KCNA

Tun da sanyin safiyar wannan Asabar  Amirka da Koriya ta Kudu sun gudanar da wani atisayen sojoji na hadin gwiwa inda suka harba wasu makamai masu linzami. Wannan na zuwa ne bayan wani taro da shugabannin sojojin kasashen biyu suka gudanar inda suka tattauna batun yiwuwar daukar matakan sojan kan koriya ta Arewar. 

Wannan dai shi ne karo na farko da kasashen biyu suka bayyana yiwuwar amfani da karfin sojan kan Koriya ta Arewar wacce ga al'ada sukan mayar mata da martani ta hanyar harba makamai masu lizzami kawai.

Koriya ta Arewa ta sanar da mallakar makamin da za ta iya harar ko wani yanki na kasar Amirka, bayan da ta yi nasarar harba wani makami mai linzami da ya yi tafiyar kilomita 998 kafin ya fadi a cikin ruwan tekun Japan.