1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni: Gasar Bundesliga ta dau zafi

Gazali Abdou Tasawa MNA
November 12, 2018

Tauraruwar kungiyar Borussia Dortmund na ci gaba da haskakawa a wasannin Bundeligar kasar Jamus.

https://p.dw.com/p/387Qk
Fußball Bundesliga 10. Spieltag | Borussia Dortmund v Bayern München | Tor zum 3:2
Hoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz

A cikin shirin na yau za ku ji cewa tauraruwar kungiyar Borussia Dortmund na ci gaba da haskakawa a wasannin Bundeligar kasar Jamus, bayan da ta lallasa yaya baba Bayern Münich da ci 3-2 a wasan karan battan kishiyoi na "Clasikon" kasar Jamus a karshen mako.

-Kungiyar Esperance ta kasar Tunusiya ta lashe gasar cin kofin zakarun Afirka ta kwallon kafa bayan da ta doke takwararta ta Al-Ahlin kasar Masar.

Dan wasan gaba na kungiyar Dortmund Paco Alcacer ya ci wa kungiyarsa kwallo ta uku kuma ta karshe a wasan karan battan kishiyoyi na kasar Jamus da aka buga a ranar Asabar inda Dortmund ta karbi bakuncin Bayern Münich ta ko casata da ci uku da biyu a filin wasan na Iduna Park a birnin Dortmund a gaban 'yan kallo sama da dubu 80.

A yanzu dai Dortmund ta kara yin kane-kane a saman tebirin na Bundesliga da maki 27. Kungiyar Mönchengladbach wacce ta doke Bremen da ci uku da daya na a matsayin ta biyu da maki 23, RB Leipzig wacce ta lallasa Bayern Leverkusen da ci uku da babu na a matsayin ta uku da maki 22. Bayan nasarar da ta samu da ci uku da babu a gaban Kungiyar Schalke 04, Frankfurt na a matsayin ta hudu da maki 20, a yayin da Bayern Münich ke a matsayin ta biyar da maki 20.

A Afirka kuwa Kungiyar Esperance ta kasar Tunusiya ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na zakarun Afirka bayan da ta doke takwarta ta Al-Ahlin kasar Masar da ci uku da nema a wasa na biyu na karawar karshe da ta gudana a ranar Juma'ar da ta gata a birnin Tunis.