1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin makamashin nukiliyar Koriya ta Arewa

December 20, 2010

Koriya ta arewa, ta sassauta a batun shirin ta na makamashin nukiliya

https://p.dw.com/p/Qgya
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong IlHoto: AP Graphics

Koriya ta Arewa ta ce a shirye ta ke ta bar jami'an ƙungiyar da ke kula da makamashin nukiliya su dawo ƙasar su binciki cibiyar makamashin nukiliyar ta. Rahotanni sun rawaito cewa wannan sanarwar ta zo ne a yayin da Bill Richardson wani tsohon jami'in diplomasiyyar Amurka ke ziyara a ƙasar. Koriya ta Arewar ta amince da Richardson cewa Jami'an hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya su koma gurin da take sarrafa makamashin a garin Yongbyong.

Ta kuma sake amincewa da a fitar da garewanin makamishin Uranium 12,000 kana ta amince da ƙirƙiro wata hukumar da zata inganta sadarwa tsakanin Koriyawan da kasar Amurka. A watan da ya gabata ne Koriya ta Arewa ta sanar da cewa ta kafa wata cibiya ta inganta makamashin uraniyum ɗin ta, lamarin da ya jefa ƙasashe da dama cikin fargabar cewa ƙasar na iya amfani da cibiyar domin sarrafa bama-baman ƙare dangi.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Umaru Aliyu