A cikin shirin za ku ji cewa gwamnatin kasar Jamus ta baiwa Najeriya da ma kasashen Ecowas taimako na euro milyan 5.5 domin yaki da cutar covid 19, a daidai lokacin da asusun bada lamuni na duniya ya amince a baiwa Najeriya taimakon gaggawa na dalla bilyan 3.4 domin yaki da wannan annobar.