A cikin shirin za a ji cewa, a Najeriya gwamnati ta dakatar da aiwatar da wasu jerin haraji da kasar ta sanya. A Nijar kuma, kungiyar EU ce ke shirin bai wa kasar tallafi domin taimakawa fannin tsaro da kuma illimi. A Kamaru ana bayar da rigakafin bakon dauro sakamakon yadda cutar ta kama dubban yara.