Shirin rufe tashar nukiliyar Koriya ta arewa
July 14, 2007Talla
Jamian binciken na hukumar makamashin nukiliya ta majalisar ɗinkin duniya sun sauka Koriya ta arewa a matakin fara aiwatar da shirin rufe babbar tashar nukiliyar ta dake yongbyon. Wannan dai shine karon farko da jamián binciken suka kai ziyara cibiyar tun cikin shekara ta 2002. A waje ɗaya kuma sahun farko na mai da aka yiwa Koriya ta arewan alƙawari ya isa ƙasar. A yau da sanyin safiya jirgin ruwan koriya ta kudu dake dauke da man ya sauka tashar jiragen ruwa na koriya ta arewa. A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka cimma, Koriya ta arewa tace zata rufe tashar nukiliyar ta Yonbiyon da zarar ta sami man da aka alakawurta mata daga makwabciyar ta koriya ta kudu.