A labaran duniya na cikin shirin za a ji cewa kotun kolin Jamus ta ba da umurnin bude masallatai da sauran wuraran ibada da aka rufe a dalilin Coronavirus, tana mai cewa matakin ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar. Sai dai ta sa sharadin daukar matakan kariya.